Amirka ta ce a gaggauta sakin Bazoum
July 29, 2023Talla
Blinken da ke kammala ziyarar aikinsa ta kasashen yankin Pacific, ya ce Amirka za ta bai wa shugaba Bazoum dukannin wani goyon bayan da yake bukata.
Babban jami'in na Amirka ya kuma yabawa rawar da shugaba Bazoum ya taka wajen wanzar da zaman lafiya, ba a Nijar kadai ba har zuwa sauran kasashen da ke yammacin Afirka.
Blinken ya ce ci gaba da tsare shugaban na barazana ga hadin kai tsakanin kasashen biyu da aka kwashi tsawon shekaru da kullawa da ma daruruwan miliyoyin tallafi ga Nijar din.
Tuni da Blinken ya gana da ministar harkokin wajen Faransa kan halin da Nijar ke ciki, inda ya jadadda bukatar gaggauta mayar da kasar kan tafarkin kundin tsarin mulkin kasar.