1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta ce Rasha na kwashe dukiyoyi a Afirka

October 7, 2022

Amirka ta zargi sojojin hayan Rasha da ke ayyukan samar da tsaro a wasu kasashen Afirka da amfanin da damar kasancewarsu a kasashen wajen kwashe albarkatun kasa.

Jakadiyar Amirka a Majalisar Dinkin Duniya, Linda Thomas-Greenfield
Hoto: DAVID DEE DELGADO/REUTERS

Amirkar ta ce sojojin na haya na kamfanin Wagner na kwashe albarkatun ne a kasashen Jamhuriyar Afirka ta tsakiya da Mali da Sudan da ma wasu yankunan Afirkar, inda Rasha ke amfani da su wajen samun kudaden taimaka mata a yakin da take yi a Ukraine.

Jakadiyar Amirka a Majalisar Dinkin Duniya, Linda Thomas-Greenfield, ta ma ce Rasha na amfani da kudaden a wasu yake-yaken da take yi a wasu wasu yankunan a Afirka da ma wasu na kasashen Larabawa.

Jakadiyar ta Amirka ta kuma ce sojojin hayan Rashar, na take hakkin bil Adama a ayyukan da suke yi cikin kasashen.

Sai dai Rasha a nata bangaren ta yi watsi da zargin na Amirka, tana mai bayyana shi a matsayin wani shiryayyen abu da aka yi domin taba manata kima.