Amirka ta ce ya zama wajibi a dauki wani mataki a Darfur
September 23, 2006Talla
Gwamnatin Amirka ta fara wani sabon yunkuri da nufin gano hanyar girke dakarun MDD a lardin Darfur mai fama da rikici dake yammacin kasar Sudan. Sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice ta fadawa wani taron ministoci a gefen taron babbar mashawartar MDD a birnin New York cewa dole ne a dauki wani mataki akan yankin na Darfur.
Rice ta ce “Idan manufar mu shi ne daukar nauyin kare mafi rauni da marasa karfi a cikinmu, to dole mu rabu da fatar baka, mu dauki sahihan matakai a Darfur.”
A karshen watan agusta dai kwamitin sulhun MDD ya zartas da kuduri mai lamba 1706 wanda ya tanadi girke sojojin majalisar su dubu 17 da ´yan sanda dubu 3 don maye gurbin dakarun kiyaye zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afirka a Darfur.