1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta daina bai wa Nijar tallafi

Abdourahamane Hassane
October 10, 2023

A karon farko a hukumance Amirka ta bayyana mamayar da sojoji suka yi na madafun iko a Jamhuriyar Nijar a watan Yulin da ya gabata a matsayin juyin mulki .

 Abdourahamane Tiani
Abdourahamane TianiHoto: ORTN/Télé Sahel/AFP

Wani babban jami'n gwamnatinAmirka ya ce sun yanke shawara daina bai wa Nijar kudaden tallafi saboda a cikin watanni biyun da suka gabata sun bi duk hanyoyi da suka dace ba tare da cimma nasara ba, na ganin sojojin sun tabbatar da tsarin mulki na dimukaradiyya da suka hambarar, inda ya ce sakamakon haka  Amirka ta kawar da ba da  dala miliyan 442 na taimakon tattalin arziki ga Nijar. Babu dai wani karin bayyani da jami'in na Amirka ya yi bayan bayyana sanarwa dakatar da ba da tallafin kudin ga Nijar.