Amirka ta fara gudanar da bincike akan rahoton kone ´yan Taliban da sojojinta suka yi
October 21, 2005Talla
Amirka ta nuna kaduwa game da rahotannin da aka bayar cewa sojojin ta sun kone gawawwakin wasu mayakan Taliban a Afghanistan. Wani kakakin ma´aikatar harkokin waje a Washington ya jaddada cewar za´a hukuntan sojojin da suka aikata wannan danya idan aka tabbatar da aikata wannan laifi. Gidan telebijin Australiya SBS ya rawaito cewar dagangan wasu sojojin Amirka suka kone gawawwakin ´yan Taliban biyu kuma suka hana a yi musu jana´iza ta musulunci, sannan kuma daga bisani suka razanar da mazauna wani kauye dake kusa. Hakan dai ya karya dokokin kudurin birnin Geneva.