1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya: Faragaba bayan soma kwashe sojoji

Ramatu Garba Baba
October 7, 2019

A wannan Litinin aka soma ganin rundunar sojin Amirka na ficewa daga yankin Arewacin kasar Siriya bayan da Turkiyya ta sanar da shirin afkawa 'yan tawayen da ke barazana ga zaman lafiyarta.

Syrien Manbij US Soldaten
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Shugaba Donald Trump ya ce babu amfanin kasancewa a cikin yakin da aka gagara samun nasara bayan yana lakume kudin kasar. Kungiyar mayakan Syrian Democratic Forces da Amirka ke jagoranta ta baiyana damuwa inda ta ce sam hakan bai dace ba. Wannan na zuwa ne bayan wata sanarwar gwamnatin kasar Turkiyya na afkawa yankin don karya lagon mayakan Kurdawa da IS da suka kasance barazana ga zaman lafiyar kasar.

A nata bangaren kuwa, Kungiyar Syrian Observatory for Human Rights da ke rajin kare hakkin dan Adam mai mazauni a Birtaniya, ta ce matakin Amirkan ya jefa Siriya cikin wani munmunan babi, ta yi fargabar za a tsinci kai cikin tashin hankalin da ba a taba gani ba a kasar ta Siriya.