1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Amirka ta gargadi Isra'ila a kan kai hari Iran

Binta Aliyu Zurmi
October 5, 2024

Shugaba Joe Biden na Amirka ya gargadi mahukuntan Isra'ila a kan kauce wa kai hari a cibiyoyin man kasar Iran. Biden ya ce Isra'ila kar ta manta da irin goyon bayan da Amirka ke ba ta.

USA | Präsident Joe Biden Pressekonferenz in Washington D.C.
Hoto: AFP via Getty Images

Shugaba Biden na mai cewa yanzu haka yana kokarin hada kan shugabannin duniya ne domin gudun barkewar yaki a yankin Gabas ta Tsakiya.

Wannan kiran da na zuwa ne a daidai lokacin da tsohon shugaban Amirka Donald Trump ya ce Isra'ila ta hanzarta daukar fansa ta hanyar kai wa tashar makamashin nukiliyar Iran hari.

Biden wanda bai ji dadin wadannan kalaman na Trump ba , ya ce Isra'ila kar ta manta da irin goyon bayan da Amirka ke bata yayin yanke shawara a matakai na gaba da za ta dauka.

Isra'ila ta sha alwashin daukar fansa a kan harin rokoki da Iran din ta yi mata a farkon makon nan.

 

Karin Bayani: Yankin Gabas ta Tsakiya ya shiga rudani