1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta gayyaci jami´an Majalisar Dinkin Duniya zuwa sansanin Guantanamo

October 29, 2005

Amirka ta gayyaci wasu wakilan MDD zuwa sansaninta na Guantanamo inda ta ke tsare da mutanen da ta ke zargi da aikata ta´addanci. Wata sanarwa da ma´aikatar harkokin waje a birnin Washington ta bayar ta nunar da cewa za´a bawa masanan na MDD damar ganewa idonsu halin da mutanen da ake tsare da su a wannan sansani ke ciki, musamman bayan zargin da ake yi cewa ana keta hakkin su. Tun kimanin shekaru 4 da suka wuce jami´an MDD ke neman Amirka ta ba su izinin kai ziyarar ganewa ido a sansanin na Guatanamo dake kasar Cuba.