1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta gindaya sharudda don sabunta yarjejeniyar Iran

Yaya Azare Mahamud
May 22, 2018

Ana ci gaba da martini kan sharudda 12 da Amirka ta gindaya kan kasar Iran, kafin ta sabunta yarjejeniyar nukiliya lokacin da Amirka ke barazana bisa kakaba takunkumi kan kasar ta Iran mafi tsanani a tarihi.

Mike Pompeo US Außenminister
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. S. Applewhite

 

Sharudda 12  masu wuyar aiwatarwa da Sakataren harkokin wajen Amurka na Mike Pompeo,  ya gindayasu  kafin a sabunta yarjejeniyar nukiliya da Iran, sun kunshi  matakan karya bakalin kasar ta Iran a bangaren sojoji da karya bakalin tasirinta na diplomasiyya a yankin. Pompeo ya kuma ja kunnen kasashen Turai da kamfanoninsu da ke son ci gaba da hulda da Iran, wadandan ya ce idan suka bijire wa matakin na Amurka, to kuwa su ma za su yaba wa aya zaki.

Hoto: picture alliance/AP Photo/Iranian Presidency Office

Tuni dai  shugaban Iran, Hassan Rouhani, wanda ya nemi kasashen Turai da su karfafa alakarsu ta kasuwanci da ita,ya yi watsi da wannan barazana.

A yayin da kasashen Saudiyya da Daular Larabawa da Baharain suka siffanta sharuddan da wadanda aka jima ana jira, suka kuma wajaba da a aiwatar da su sau da kafa. Ita kuwa Shugabar kula da harkokin kasashen waje ta kungiyar Tarayyar Turai, Federica Mogherini cewa ta yi  "Babu abin da zai hana kasashen kungiyar ci gaba da mutunta yarjejeniyar nukiliyar Iran, duk da takunkuman da Amurkan ke barazanar sake kakaba wa kamfanonin kasashen na Turai a kan Iran.”

Hoto: picture-alliance/Photoshot

Sakataren harkokin wajen kasar Birtaniya Boris Johnson ya siffanta sharuddan da na gagara badau, yana mai nuna takaicinsa da yin fatali da tsohuwar yarjejeniyar da Amirka ta yi, wacca ya ce ta taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya da habakar hada-hadar kasuwanci.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani