Amirka ta ja hankalin Rasha kan Ukraine
January 8, 2022Gabanin tattaunawar da za a yi a mako mai zuwa da Rasha game da makomar Ukraine sakataren harkokin wajen Amirka Anthony Blinken ya ce har yanzu yana ganin akwai dama ta samun masalaha ta diflomasiyya ga rikicin na Ukraine sai dai ya zargi Rasha da jibge sojoji kusa da kan iyakar Ukraine.
Tsawon makonni ana baiyana fargaba a Ukraine da jibge sojojin da Rasha ke yi.
A shekarar 2014 Rasha ta kwace yankin Crimea na Ukraine ta shigar da shi cikin kasarta yayin da ta rika bada goyon baya ga kungiyoyin aware a gabashin Ukraine.
Jibge sojojin ya haifar da fargabar cewa Rasha na iya sake kwace wasu yankunan Ukraine.
Shugaban Amirka Joe Biden tuni ya gargadi shugaban Rasha Vladimir Putin kan wannan mataki.
Putin ya mayar da martani da bukatar sojojin kungiyar kawancen tsaro ta NATO su ja baya daga yankin kasar Rasha.