1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta kakkabo makami mai linzami na mayakan Houthi

January 15, 2024

Rundunar sojin Amirka ta ce ta kakkabo wani makami mai linzami da mayakan Houthi suka harba daga Yemen zuwa kudancin tekun Bahar Maliya.

Jirgin Amirka da ke kokarin dakile hare-haren 'yan Houthi a tekun Bahar Maliya
Jirgin Amirka a kokarin dakile hare-haren 'yan Houthi a tekun Bahar MaliyaHoto: US Central Command via X/REUTERS

Rundunar ta ce an harba makami mai linzamin ne zuwa wani jirgin ruwan sojin Amirka a ranar Lahadi. An dai kakkabo makamin ne a kusa da tashar ruwan Hudaida da ke Yemen.

Babu rahoton asarar rayuka ko barna. A baya-bayan nan Amirka da kuma kawayenta dai sun kaddamar da jerin hare-hare kan 'yan tawayen na Houthi da suke zafafa kai hare-hare kan jiragen ruwa na kasuwanci a Bahar Maliya. Sai dai mayakan sun sha alwashin daukar fansa.

Karin bayani:  Bahar Maliya: Takaddamar Amurka da Houthi

Kungiyar Hezbollah ta ce farmakin da Amurka da mukarabbanta ke kai wa kan 'yan Houthi na Yemen ba komai zai janyo ba, face haddasa rincabewar rikicin yankin.

Karin bayani:  Dalilan 'yan Houthi na barazana a Bahar Maliya 

Tun bayan barkewar rikici a Zirin Gaza a watan Octobar bara, mayakan na Houthi da ke da iko da yawancin yankunan kasar Yemen ke kai hare-hare da jirage marasa matuka da kuma makamai masu Linzami mussaman kan Isra'ila.