Amirka ta kashe jagoran al-Qaida a Yemen
June 16, 2015Jagoran kungiyar al-Qaida a kasar Yemen wato Al-Washihi ya halaka a cikin wani hari da wani jirgi marasa matuki wato Drohn na kasar Amirka ya kaddamar a wata maboyarsa. Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP ya ce kungiyarsa ta Aqpa ce ta tabbatar da wannan labari a cikin wani faifayen bidiyo da ta wallafa a ran Talata inda ta ce ya rasu ne tare da wasu na hannun damarsa su biyu.
Tuni kuma ta ce ta maye gurbinsa da wani mai suna Qassem al-Rimi. Ana dai kallon al-Washihi dan shekaru 37 a duniya a matsayin mutun da ke rike da matsayi na biyu a cikin kungiyar al-Qaida a duniya, kuma mutuwarsa babbar asara ce ga reshen kungiyar ta kasar Yemen.
Shi ne dai ya dauki alhakin harin ta'addancin da aka kai a kamfanin jaridar kasar Faransa ta Charlie Hebdo da ma yinkurin kai hari a wani jirgin jigilar fasinja na kasar Amirka ranar sallar Krismeti a shekara ta 2009.