1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta kashe wani jigon IS a Somaliya

January 27, 2023

Dakarun musamman na Amirka a Somaliya sun kashe shugaban kungiyar IS na yankin arewacin kasar a wani samame da suka kai.

Jami'in sojan Amirka a Somaliya
Hoto: Tech. Sgt. Christopher Ruano/AP Photo/picture alliance

Hukumomi a Somaliya na cewa, dakarun musamman na Amirka da ke kasar sun kashe wani jigon kungiyar IS a samamen da suka kai wani kogo da ke arewacin kasar.

Bilal al-Sudani ya kasance shugaban kungiyar a yankin, kana mai taka rawa ga fannin sadarwar kungiyar a cewar sakataren tsaron Amirka Lloyd Austin.

A cikin sanarwar da ya fitar, Austin ya ce, wannan mataki ne da ya sanya Amurka da kawayenta cikin karin kwanciyar hankali, kuma hakan wata alama ce ta tsayin daka wajen kare Amurkawa daga barazanar  'yan ta'adda.

Sanarwar ta kara da cewa, shugaba Joe Biden ne ya bayar da umurnin kai harin wanda ya yi sanadiyar mutuwar al-Sudani da wasu mayakan kungiyar 10.

Rahotanni na nuni da cewa babu fararen hula da aka kashe ko suka ji rauni yayin kaddamar da harin.