Takaddamar Amirka da Iran
June 23, 2021Wata sabuwar takaddama ta kunno kai a tsakanin kasashen Amirka da Iran, bayan wani mataki na ba-za-ta da Amirka ta dauka na kwace wasu shafukan yada labarai na intanet da take zargi da yada labaran karya. Daga ciki akwai wadanda na 'yan tawayen Houthi a Yemen ne da Iran din ke goyon baya.
Cikin shafuka kimanin talatin da uku da ma'aikatar shari'a a Amirkan ta ce ta kwace, sun hada da shafukan Intanet da Kungiyar ma'aikatar Rediyo da Talabijin na jamhuriyar Musulunci da kasar ta Iran ke jagoranta. Wannan dai, ya janyo tsaiko ga dimbin masu mu'amala da shafukan da suka gagara samun labarai da ake wallafawa a wadannan shafukan.
Kawo yanzu, gwamnatin Iran ba ta mayar da martani ba. Sabuwar takaddamar na zuwa ne a yayin da kasashen biyu ke kai ruwa rana kan batun sabunta yarjejeniyar nukiliya da Iran.