Amirka ta nuna damuwa ga hukuncin kisa a Masar
March 24, 2014Wata kotu da ke lardin Minya na kudancin kasar Masar ta yanke hukunci kisa ga mutane 529 wadanda mafi yawansu magoya bayan hambararren shugaban kasar Mohammed Mursi ne. Wannan hukuncin shi ne wani hukunci na gama gari mafi girma a tarihin kasar na wannan zamani. Hukuncin ya kuma zo ne daidai lokacin da ake ci gaba da murkushe magoya bayan Mursi tun bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatinsa a watan Yulin bara. Gwamnatin Amirka ta ce ta damu matuka ga hukuncin kisan tana mai saka ayar tambaya ga sahihancin zaman shari'ar da aka yi wa mutane masu yawa cikin kwanaki biyu kacal. Sai dai gwamnatin rikon kwaryar kasar da sojoji suka dorata kan karagar mulki, ta kare hukuncin kotun da cewa an yanke wa mutanen hukuncin ne bayan wani nazari mai zurfi kuma ma suna da 'yancin daukaka kara. Mutane 150 daga cikin wadanda ake tuhuma suka gurfana gaban kotun, yayin da saura aka yanke musu hukunci a bayan idonsu. Daga ciki kuwa har da jagororin kungiyar 'Yan uwa Musulmi da yanzu aka haramta ayyukanta. An zargi mutane da gudanar da wata mummunar zanga-zanga da ta yi sanadiyar mutuwar wani babban jami'an dan sanda.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar