1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabar kotun kolin Amirka ta rasu

Abdoulaye Mamane Amadou
September 19, 2020

Shugaban Amirka Donald Trump ya ce ya kadu da jin labarin rasuwar Ruth Bader Ginsburg shugabar babbar kotun kolin kasar da Allah Ya yi wa cikawa a ranar Juma'a.

USA Ruth Bader Ginsburg 2019
Hoto: Cliff Owen/dpa/picture-alliance

Ana yiwa maragianyiya Ruth Bader Ginsburg kallon cikakkiyar 'yar rajin kare doka da oda uwa uba da 'yancin mata a kasar, lamarin da ya kai shugaba Donanld Trump da jinjinawa rayuwarta yana mai bayyana cewa ta nuwa jan namijin kokari.

Tuni fadar White House da majalisar dokokin kasar suka bayyana sasauta tuta a wani mataki na jimamin rasuwar, kana kuma jama'a da dama na ci gaba da nuna alhinin rasuwar shugabar kotun inda suka yi dafifi a harabar kotun tare da kunna kyandura da ajiye furanni.

Mai shekaru 87 a duniya Ruth Bader Ginsburg ta rasu ne a yammacin jiya bayan tayi fama da rashin lafiya, to amma sai dai kuma mutuwar ta na zuwa ne a daidai lokacin da ake dab da gudanar da zaben kasar.