1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Amirka ta sake gargadin Rasha a kan Ukraine

December 31, 2021

Amirka ta sake yi wa kasar Rasha kashedi game da jibge dakarunta a arewacin kasar Ukraine. Sannan ta yi barazanar daukar manyan matakai a kan Rasha muddin ta yi gaban kanta.

USA Russland Kombo Joe Biden und Putin
Hoto: Eric Baradat/Pavel Golovkin/AFP

Shugaba Joe Biden na kasar Amirka ya sake gargadin takwaransa na Rasha Vladimir Putin a game da take-takensa na mamaya a Ukraine. Cikin wata tattaunawa ta wayar tarho, Shugaba Biden ya shaida wa Putin cewa Amirka da kawayenta za su dauki matakai masu tsanani muddin ya yi kunnen kashi a kan batun na Ukraine. A cewar Biden Rashar na iya fuskantar takunkumai ciki har da na tattalin arziki idan ta kama.

A nata bangaren kasar ta Rasha gargadi ta yi game da takunkuman da Amirka ke fadi, wadanda ta ce in har aka yi za a tafka babban kuskure, kamar yadda wani mai bai wa Shugaba Putin shawara ya fada. Sai dai Amirka ta nuna fatan Rashar na iya kwance damarar yakin.