1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Amirka ta shawarci Sudan kan zaman lafiya

Ramatu Garba Baba MNA
April 5, 2021

Amirka ta shawarci gwamnatin Sudan da ta kara azama don ganin ta cimma cikakkiyar yarjejeniyar zaman lafiya da kuma warware takaddama a tsakanin kasar da Habasha kan gina madatsar ruwan Kogin Nilu.

Sudan Khartum | Steven Mnuchin, US-Finanzminister | Abdullah Hamdok, Premierminister
Hoto: Marwan Ali/AP Photo/picture alliance

A wata tattaunawa a tsakanin Firaiminista Abdallah Hamdok da Sakataren harkokin wajen Amirkan Antony Blinken, Blinken ya shawarci samar da damar shimfida tsare-tsaren inganta sauye-sauye a kasar da ta sha fama da zanga-zangar neman sauyi, bayan kifar da gwamnatin Oumar Hassan al-Bashir na sama da shekaru talatin.

Hakazalika sun tabo batun takaddamar kasar ta Sudan da Habasha kan shirin Habashan na gina madatsar ruwa a kan kogin Nilu, wanda tuni ake ganin barazana ce babba ga kasashen yankunan da ke zagaye da kogin. Suna dai fuskantar matsin lamba daga kasashen waje kan su cimma yarjejeniya guda mai ma'ana bayan kasa cimma matsaya a duk yunkurin baya.