Amirka ta shawarci da a tallafawa Ukraine
February 8, 2015Ga mutane da dama tun da aka fara taron tsaro na kasa da kasa a birnin Munich a shekara ta 1963 na bana ne ya fi tsauri sosai. Jagoran taron na bana Wolfgang Ischinger, ya fadawa kamfanin dillancin labaran Jamus cewa taron wanda suka kammala a yau lahadi, ya kasance haka ne domin kusan a ce babu wani labari mai dadi da suka tattauna.
Wadannan labarai marasa dadi dai sun hada da rikicin Ukraine da 'yan awaren da ke goyon bayan Rasha, abin da kuma aka tattauna a taron a matakai daban-daban. Garin tattaunawar ma wakilan taron sun shiga wani yanayi na cacar baki da musayar kalamai marasa dadi bayan da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya gabatar da jawabinsa. Mahalartar ma sun fashe da dariya bayan da ya ce anshe yankin Kirimiya da Rasha ta yi, ta yi shi ne bisa tanadin dokokin Majalisar Dinkin Duniya, Sai dai a karshen taron John MaCain sanata a Majalisar dokokin Amirka ya bukaci da a tallafawa Ukraine da makaman kare kai, inda ya kara da tambayar ko yaushe Putin zai ba da hadin kai a kawo karshen yakin da har yanzu ya ce zargin ba ya faruwa.