1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Amirka ta nemi a yi sulhu a Gabas ta Tsakiya

Ramatu Garba Baba
January 30, 2023

Amirka ta yi kira ga mahukuntan Isra'ila da Falasdinu kan su kai zuciya nesa su nemi mafita daga rikicin da ke barazana ga tsaron yankin Gabas ta Tsakiya.

Hoto: Stefani Reynolds/REUTERS

Sakataren harkokin wajen Amirka ya yi kira ga Isra'ila da Falasdinu kan su kai zuciya nesa a sakamakon yadda rikici a tsakaninsu ke kara kazancewa. Jami'in da ke ziyarar aiki a kasashen yankin Gabas ta Tsakiya ya ce, akwai bukatar bangarorin biyu su sake nazari su koma kan teburin tattaunawa don wanzuwar zaman lafiya. Sakatare Blinken ya gana da Firaminista Benjamin Netanyahu a birnin Tel-Aviv kafin daga bisani ya yada zango a yankin Falasdinu da kasar Jordan a wannan makon.

Rikici a tsakanin makwabtan biyu ya kara tsananta a sakamakon wani hari mai kama da na ramuwar gaya da wani yaro Bafalasdine mai shekaru goma sha uku da haihuwa ya kai wani wurin ibada inda ya hallaka Yahudawa bakwai, kwanaki kalilan bayan wani samame da sojojin na Isra'ila suka kai kusa da wani yanki da ta mamaye inda mutum tara suka mutu a harin na Jenin.