Amirka ta soma aiki da sabon haraji kan Chaina
August 23, 2018Da wannan sabon karin haraji wanda ya kai na miliyan dubu 16 na Dalar Amirka, kasar ta Amirka ta dora a jumulce harajin miliyan dubu 50 na Dalar Amirka kan hajojin kasar ta Chaina da ke shigowa kasar.
Sai dai kuma jim kadan bayan da Amirka ta soma aiki da wannan mataki ita ma kasar ta Chaina ta mayar da martani ta hanyar dora sabon harajin fito na kimanin Dalar Amirka miliyan dubu 16 kan hajojin kaar ta Amirka da ke shiga kasarta.
A karkashin wannan takun saka dai kasar ta Amirka ta yi barazanar yiwuwar kara dora wani sabon harajin na kimanin miliyan dubu 200 na Dalar Amirka kan hajojin kasar ta Chaina a watan Satumba mai zuwa.
Shugaba Donald Trump ya dauki wannan mataki ne kan kasar ta Chaina da nufin ladabtar da ita a bisa zargin da yake yi mata na ha'intar kasarsa a cikin huldar kasuwancin da ta hada kasashen nasu.
Wannan mataki na Amirka na zuwa ne a daidai lokacin da a wannan Alhamis wakillan kasashen biyu suka shiga kwana na biyu na tattaunawar a birnin Washington da nufin gano bakin zaren warware matsalar.