Gargadin Amirka kan balaguro a Burkina Faso
November 27, 2019Talla
A cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta fitar a jiya Talata ta ce a yanzu kasar ta Burkina Faso ta kai kololuwar hadari ga matafiya. A shekarun baya dai Burkina Faso na daga cikin kasashen da 'yan yawan buda ido ke yawan kai ziyara.
To sai dai tun daga shekara ta 2015, ana fuskantar sace-sacen jama'a ko yin garkuwa da su don neman kudin fansa, da ma hare-haren kungiyoyin masu da'awar jihadi.
MDD ta kiyasta cewa daga farkon shekara ta 2015 zuwa yau, Mutane kimanin 700 suka halaka wasu kimanin dubu 500 suka tsere daga gidajensu a kasar ta Burkina Faso a sakamakon hare-haren kungiyoyin 'yan ta'adda.