Amirka ta yi martani kan umurnin kotun duniya
October 3, 2018Talla
Bayan umurnin da kotun duniya ta bai wa Amirka na ta janye takunkuman tattalin arziki da ta kakaba wa Iran, gwamnatin Shugaba Donald Trump, ta ce za ta dakatar da dadaddiyar yarjejeniyar nan ta kawance da Iran din.
Ana dai kallon hakan a matsayin sake dagulewar lamura tsakanin fadar White House da kuma mahukuntan birnin Tehran.
Ministan harkokin wajen Amirka Mike Pompe, ya ce ba tun yau ba ne ya kamata a dakatar da yarjejeniyar da aka sanya wa hannu a shekara ta 1955.
Amirka ta kakaba takunkuman a kan Iran ne saboda rigimar nan ta mallakar makamashin Nukiliya.
Kuma a cikin watan Yulin bana Iran ta shigar da karar Amirkar a gaban kotun ta duniya, inda ta kalubalanci sake sanya mata takunkuman, da ke da illa ga tattalinta na arziki.