Pompeo zai gana da hukumomin Turkiyya
October 17, 2018Dan asalin kasar ta Saudiyya Jamal Khashoggi, ya yi batan dabo tun bayan da ya shiga karamin ofishin jakadancin kasar ta Saudiyya a birnin Istanbul a ranar biyu ga wannan wata na Oktoba. Ana dai zargin hukumomin na Saudiyya da laifin hallaka dan jaridan Khashoggi mai shekaru 59 da haihuwa a karamin ofishin jakadancin na Saudiyya da ke Istanbul. Sai dai kuma kasar ta Saudiyya na ci gaba da musanta wannan zargi. Da yake magana kafin ya bar birnin Ryad da safiyar wannan Larabar Mike Pompeo cewa ya yi:
"An tabbatar da cewa za a gudanar da bincike na hakika babu son kai, bayan wannan tattaunawa da muka yi, za a samu gano bakin zaran wannan matsala, tare da sanin dunakkin wadanda nauyin wannan lamari ya rataya a kan su, har ma nauyin da ya rataya a kan hukumomi na saudiyya daga koli."