Amirka: Tim Walz ya sha alwashin lallasa Trump
August 22, 2024Talla
Tim Walz ya sha alwashin cewa da shi da abokiyar takararsa Kamla Harris za su yi nasara kan abokin hammayarsu na jam'iyar Republican a babban zaben Amirka na watan Nuwambar 2024.
A jawabinsa a yayin babban taron jam'iyar a birnin Chicago, gwamnan jihar Minnesota, Tim Walz ya ce wannan babbar dama ce a gare shi na zama abokin takarar Kamla Harris.
Karin bayani: Zaben Amirka: Wacece Kamala Harris?
Walz ya kuma soki manufofin jam'iyyar Republican ta Donald Trump, ya na mai cewa abun da Amirkawa ke bukata shi ne ababen da za su samar da ci gaba ga rayuwarsu. Walz ya kara da cewa, gwamnatin Trump ba za ta amfani kowa ba, face attaijirai da kuma masu tsattsaurar ra'ayi.