SiyasaArewacin Amurka
Za a bude shari'ar wanda ake zargi da kisan George Floyd
March 7, 2021Talla
A ranar Litinin ake sa ran fara zabar alkalai a birnin Minneapolis da za su saurari shari'ar da za a yi wa Derek Chauvin da aka nada a hotan bidiyo ya danne wuyan bakar fata Floyd da gwiwarsa har sai da ya ce ga garinku, lamarin da ya haifar da zazzafar zanga-zanga a ciki da wajen Amirka.
Rahotanni sun ce shari'ar na bukatar samun gogaggun alkalai saboda sarkakiyarta, za a rinka watsa ta kai tsaye sannan za a samar da tsaro a harabar kotun da za a saurari karar.
A ranar 29 ga watan na Maris ake sa ran za a fara fafata shari'ar amma sai karshen watan Afrilu ake sa ran samun kammalallen hukuncin da kotu za ta yanke a kan lamarin kisan George Floyd.