1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka za ta kafa rundunar sojin sama jannati

Gazali Abdou Tasawa
December 18, 2018

Kasar Amirka na shirin kafa wata sabuwar rundunar soji ta sama jannati wacce za ta dauki nauyin kula da harakokin bincike na sararin samaniya na ma'aikatar tsaron kasar ta Pentagon. 

Kasachstan Start Sojus-Rakete | Astronauten David Saint-Jacques & Oleg Kononenko & Anne McClain
Hoto: Reuters/D. Lovetsky

A wani sako da Shugaba Donald Trump ya aika wa ministan tsaron kasar ta Amirka Jim Mattis da kuma fadar White House ta wallafa, ya umurci ministan da ya ba da sunan wani daga cikin manyan sojojin kasar da ya dace a nada a shugabancin wannan rundunar soji ta saman jannati ta kasar ta Amirka.

Kafa wannan runduna na a matsayin wani babban ci-gaba wajen cimma burin da Shugaba Trump ya sa a gabansa na samar da rundunar sojojin sama jannati a kasar. Sai dai kuma masu lura da harakokin siyasar kasar ta Amirka na ganin wannan shiri na iya fuskantar adawa daga majalisar dokokin kasar ta Amirka wacce ita ce ke da hurumin amincewa da kudaden girka wannan runduna.