Hong Kong: Amirka za ta shiga tsakani
November 21, 2019Talla
Tuni aka gabatar da kudurin a gaban Shugaba Donald Trump, inda ake jiran ya rattaba hannu. Idan har an tabbatar da dokokin biyu, za a dakatar da sayarwa gwamnatin Hong Kong din makamai musanman alburusan da take amfani dasu kan masu boren. Akwai kuma batun taka wa Chaina birki kan rawar da take takawa a rikicin kasar, batun da ake ganin ka iya shafar dangantakar kasuwanci a tsakanin Amirkan da Chainan.
Fiye da wata biyar kenan da zanga-zanga ta barke a yankin, rahotannin na nuni da cewar 'yan sanda na ci gaba da yi wa jami'ar babban birnin yankin kawanya, inda suke jiran masu zanga-zanga da suka kwashi kwanaki a ginin da su mika kansu.