Amirka za ta naɗa jakadi a Somaliya
June 3, 2014Wannan shi ne karo na farko da Amirka za ta naɗa wani jakadin a Somaliya a cikin shekaru 20 bayan da ƙasar ta yi fama da yaƙi. Amirka ta rufe ofishin jakadancinta da ke a birnin Mogadishu tun a shekarun 1991 a lokacin faɗuwar gwamnatin mulkin kama karya ta Mohammed Siad Barre.
An shirya a gaba shugaba Obama zai bayyana sanarwa ta tabbatar da naɗa jakadin wanda zai kasance da zama a birnin Nairobi na Kenya. Amirka wacce ta ƙaddamar da yaƙi a Somaliya a ƙarƙashin wani shinrin na MDD daga shekarun 1992 zuwa 1995. Har yanzu tana tunawa da yaƙin uku ga watan Oktoba wanda a cikinsa masu kishin addini, suka kakapo jiragen yaƙinta na sama guda byu tare da kashe sojinta guda 18. Waɗanda wasu daga cikin gawarwakin sojojin aka riƙa jansu a ƙasa a kan tittunan birnin Mogadishu.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal