Amirka za ta rage dakarun sojinta daga Jamus
June 16, 2020Talla
Ziyara da ke zuwa biyo bayan shirin shugaban Amirka Donald Trump ya fara batun janye dakarun sojin kasarsa da ke jibge a kasashen na Jamus da Poland.
Akwai sojojin Amurka kimanin dubu talatin da dari biyar, a dadin da ke zama kasa da wadanda ke girke a kasar lokacin yakin cacar baka
Mr Trump na zargin Jamus da rashin biyan isassun kudin kare kanta. Inda ya ce idan aka rage yawansu zuwa dubu 25 zai ga ko za su daidaita.
Ita kuma a nata bangaren kasar Poland na kokarin kara yawan dakarun Amirka ne a kasar ta wanda ta ce hakan na da matukar muhimmanci ga harkokin tsaronta.