Amirka za ta saka hannayen jari a Afirka
December 15, 2022Shugaban na Amirka ya yi wannan shelar ne a taron koli na shugabannin Afirka da Amirka wanda ake kammalawa a birnin Washington DC a wannan Alhamis. Biliyan 55 na dalar Amirka ne Biden ya ce gwamnatinsa za ta zuba hannayen jari a Afirka a nan da shekaru 3 da ke tafe, a kokarin dakile tasirin Chaina da Rasha a nahiyar. Dama taron na kwanaki uku na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Chaina take neman tsere wa Amirka a yawan saka hannayen jari a Afirka.
Shugaba Biden ya ce Amirka a shirye ta ke na tallafawa Afirka a duk hanyoyin da za su sami ci gaba, inda ya kara da cewar ci gaban Afirka ci gaban Amirka ne da ma duniya baki daya. A karshen taron Shugaba Biden ya yi alkawarin kai ziyara ga kasashen da ke Kudu da Hamada Sahara nan bada jimawa ba.