1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka za ta sawa China sabbin takunkumi

Abdul-raheem Hassan
March 22, 2018

Sabbin takunkumin da Amirka ke shirin sawa zai shafi manyan masana'antun kasar China da ke gudanar da ayyuka a cikin Amirka, da kuma kamfanoni da ke shigar da kayan karfe zuwa Amirka.

China Peking Xi Jinping und Donald Trump
Hoto: picture-alliance/AP Photo/A. Harnik

Fadar gwamnatin Amirka ta White house ta ce shugaba Donald Trump zai dau wadannan matakai ne bayan samun China da hannu a satar fasahar Amirka ta fannonin kere-kere ba bisa ka'ida ba. Wannan sabon takaddama dai na zuwa a dai dai lokacin da kasashen biyu ke cikin takun saka na kasuwanci, bayan da Amirka ta kirkiro da haraji kan mulmulallun karafa da Alminium da ake shigo da su kasar daga China.

A yanzu dai kasar China ta yi Allah wadai kan yadda Amirka ke kin mutunta yarjejeniyar kungiyar kasuwanci ta duniya, wannan ya sa ake ganin China za ta yi martanin ramuwar gayya kan wasu kamfanonin Amirka.