Amirka za ta sayar wa Taiwan makamai masu linzami
September 3, 2022Talla
Gwamnatin Amirka ta sanar da yiwuwar sayar wa da tsubirin Taiwan makamai masu linzami da kudinsu ya haura Euro miliyan 1000 a daidai lokacin da ake zaman tankiya tsakanin Washington da Chaina.
Ma'aikatar tsaron Amirka wace ta bayar da wannan sanarwa a yammacin Jumma'a ta ce matakin zai karfafa tsaron tsubirin Taiwan da Beijing ke ikirarin mallakinta.
Shirin sayar da makaman dai shi ne gagarumin mataki da gwamnatin Joe Biden ta amince da shi na sayar wa da Taiwan makamai duk da cewa har yanzu ana jiran sahalewar majalisar dokokin Amirka kafin Taiwan ta samu tabbacin sayen makaman na yaki.
Sai dai tuni Chaina ta gargadi Amirka cewa idan har ba ta dakatar da wannan aniya ba, to Beijing za ta bi hanyoyin da doka ta tanadar domin lalata cinikin.