Amirka za ta taimaki Turai a fannin tsaro
June 3, 2014Barack Obama wanda yake yi magana a birnin Warsaw na Poland a wani mataki na farko na ziyara da yake yi a nahiyar Turai. Ya ce Amirka za ta ware kuɗaɗe kusan biliyan ɗaya, domin aike wa da ƙarin sojojin na ruwa da na sama da na ƙasa da za ta tura a gabashin Turai sannan kuma ya ƙara da cewar.
''Ina ƙoƙarin kawo ziyara a wannan ƙasar saboda amincewa da tsaron ƙasar Poland wanda ke a matsayin tsaro na haɗin gwiwa da sauran ƙasashen Turai na gabashi da na tsakiya da ke zaman garkuwa a garemu.''
Shirin wanda na ƙarfafa harkokin soji ne tare da yin attisayi soji na haɗin gwiwa tsakanin Amirka da ƙasashen Turai za a ƙaddamar da shi da zaran 'yan majalisun Amirka sun amince da shi. Shugaba Obama dai ya kira ga shugaban ƙasar Rasha Vladmir Putin da ya yi amfanin da ƙarfin faɗa a jin da yake da shi a Yukren domin su dakatar da buɗe wuta.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu