Amirka za ta tallafa wa kasashen Afirka
August 3, 2017Talla
Wata sanarwa da hukumar ta fidda dazu ta ce za a yi amfani da dala miliyan 137 don bada tallafi a Habasha yayin da za a aike da dala miliyan 33 zuwa ga kasar Kenya don tallafa wadanda ke cikin yanayi na bukata. Wannan dai na zuwa ne bayan da watan da ya gabata Shugaba Trump din ya yi alkawarin bada tallafi na kayan abinci da kimarsu ta kai dala miliyan 639 ga kasashe irinsu Somaliya da Sudan ta Kudu da Tarayyar Najeriya da kuma Yemen wadanda wasu bangarorinsu ke fama da rikici.