SiyasaAfirka
Ethopia : Amnesty da HRW sun soki yadda ake kisan jama'a
December 16, 2021Talla
A cikin wani rahoton hadin gwiwar da suka fitar, kungiyoyin biyu sun ce a cikin watannin Nuwanba da Disamba mayakan sa kai sun hallaka dimbin fararen hula ciki har da kananan yara da tsoffi a yammacin Tigrey.
Wannan rahoton na zuwa a yayin da hukumar kare hakin bil'Adama ta Majalisar Dinkin Duniya ke shirin gudanr da taron koli na musamman kan batun cin zarafin bani Adama a yankin Tigrey, tare da duba yiwuwar kafa wani kamitin bincike na musammam a kai.
Akalla mutane miliyan biyu ne suka kauracewa gidajensu don tsira da rai tun bayan da rikici ya barke tsakanin gwamnatin tsakiya da mayakn 'yan awaren Tigrey na Habasha baya ga wasu masu dumbin yawa da suka rigamu gidan gaskiya.