1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin kashe 'yan IPOB a Najeriya

Muhammad Bello LMJ
August 5, 2021

Tun bayan da kungiyar kare hakkin dan Adam ta kasa da kasa Amnesty International ta zargi jami'an tsaron Najeriya da kisan ba gaira kan 'yan rajin kafa kasar Biafra na kungiyar IPOB, a yankin Kudu maso Gabashin kasar.

Nigeria pro-Donald-Trump-Kundgebung der Indigenous People of Biafra in Port Harcourt
'Yan kungiyar IPOB kan gudanar da zanga-zanga a ciki da wajen NajeriyaHoto: Getty Images/AFP

A rahoton na kungiyar ta Amnesty International dai, akwai bayanan cewar jami'an tsaron Najeriyar sun yi amfanin da karfin tuwo wajen kashe 'yan rajin kafa kasar Biafran na IPOB kimanin 115 a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, kungiyar kuma da Nnamdi Kanu da yanzu haka ke fuskantar shari'a a Najeriyar ke jagoranta. Wadannan kashe-kashe dai a cewar kungiyar, sun afku ne yayin da 'yan rajin kafa kasar Biafran suka matsa lamba a yankin musamman a farkon wannan shekara da mu ke ciki ta 2021.

Karin Bayani: Umarnin da IPOB ta bayar ya karbu a Najeriya

Ko da yake kungiyar ta Amnesty International ta nunar cewar a rikicin da ya afku cikin watanni hudu kacal bisa alkaluman da 'yan jaridu a Najeriyar suka bayar, yayin da adadin jami'an tsaron da suma suka rasa rayukansu ya kai 21 baya ga kone ofisoshin 'yan sanda 20 da kuma wasu ofisoshin hukumar zabe da ke yankin. Kungiyar ta kuma bayyana cewar abin da ya afku din, tsananin take hakkin dan Adam. Tuni dai 'yan kungiyar ta IPOB suka mayar da maratani kan rahoton, yayin da DW ta yi kokarin jin ta bakin jami'an 'yan sanda, sun nunar da cewa za su fitar da sanarwa dangane da rahoton.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani