1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Amnesty na son a yi bincike kan murkushe zanga-zangar Kenya

September 26, 2024

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta ce 'yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye fiye da kima tare da duka da kuma tsare masu zanga-zangar ba bisa ka'ida ba.

Jami'an tsaro sun yi amfani da karfi kan masu zanga-zanga a Kenya a watan Yuni
Jami'an tsaro sun yi amfani da karfi kan masu zanga-zanga a Kenya a watan YuniHoto: KABIR DHANJI/AFP

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta bukaci a kafa kwamiti da zai yi bincike kan murkushe masu zanga-zanga da aka yi a kasar Kenya a tsakiyar wannan shekara ta 2024. Masu rajin kare hakkin bil adama sun yi kiyasin cewa sama da mutane 50 ne aka kashe a tsakanin watan Yuni zuwa Agusta a lokacin zanga-zangar adawa da wani kudirin doka mai cike da cece-kuce. Masu jin jini a jikan sun fara gudanar da zanga-zangar cikin lumana, amma daga baya ta rikide i zuwa tashin hankali.

Karin bayani: 'Yansanda na ci gaba da afka wa masu bore a Kenya

A ranar 25 ga watan Yuni ne, 'yan sanda suka yi amfani da harsasai na zahiri a kan masu zanga-zangar da suka kutsa kai cikin ginin majalisar dokokin da ke Nairobi. Kungiyar Amnesty ta ce 'yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye fiye da kima tare da duka da kuma tsare masu zanga-zangar ba bisa ka'ida ba. Sai dai bayan wannan zanga-zanga, shugaban kasar Kenya William Ruto ya yi watsi da dokar da ta fusata matasan kasar tare da korar yawancin 'yan majalisar ministocinsa.