1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnesty: 'Yan ta'adda na amfani da yara a Nijar

Gazali Abdou Tasawa RGB
September 13, 2021

Amnesty International na zargin kungiyoyin 'yan ta’adda da daukar yara kanana aiki wajen yi musu leken asiri a yankin jihar Tillabery inda kungiyoyin suka yi kaka gida.

Amnesty international Logo
Hoto: picture-alliance/dpa/S.Kahnert

Kungiyar kungiyar kare hakkin dan Adam ta kasa da kasa wato Amnesty International ta zargi kungiyoyin 'yan ta’adda masu da’awar jihadi a yankin Sahel da daukar sabbin mayaka a tsakanin kananan yara a yankin Torodi na cikin jihar Tillabery tare da hallaka da dama daga cikin yaran. Kungiyar ta bayyana haka ne a cikin wani rahoton bincike da ta wallafa a ranar Lahadin da ta gabata. Rahoton na zuwa ne a daidai lokacin da Nijar ke fama da hare-haren 'yan ta'adda musamman a yankin na Tillabery.
Karin Bayani An kai hari a wani barikin sojin Nijar 

A cikin rahoton wanda Kungiyar Amnesty International ta rubuta da nufin jan hankalin kasashen duniya da kuma musamman gwamnatin Nijar a game da bukatar daukar matakan dakatar da wannan matsala, ta ce ta samu tabbaci daga bakin shaidun gani da ido kan yadda Kungiyar IS reshen yankin Sahara da aka fi sani da Etat Islamique au grand Sahara ko EIGS a takaice, da kuma takwararta ta GSIM wato Groupe de Soutien a l’Islam et aux musulman da ke zama reshen kungiyar Al-Qaida a yankin, na daukar sabbin mayaka a tsakanin kananan yara a cikin Jihar Tillabery, musamman a yankin Torodi da ke a yanki mai cike da hadari na magamar iyakoki uku na kasashen Mali, Nijar da burkina Faso inda kungiyoyin 'yan ta’adda suka yi kaka gida.

Karin Bayani  Farmakin sojojin Nijar kan 'yan ta'adda
Da ya ke tsokaci kan batun Malam Sadikou Moussa shugaban kungiyar EPAD mai fafutikar kare hakkin yara a Nijar ya ce, amfani da yara a cikin yaki abin assha ne. Rahoton Kungiyar ta Amnesty International ya ce, kungiyoyin ‘yan ta’addan na amfani da kananan yaran a wasu lokutan a matsayin masu yi masu leken asiri a cikin gari da ba su labarin kai kawon jami’an tsaro a yankin da ma abin da mutanen gari suke fada a game da ayyukansu. 
 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani