1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnesty ta ce a dauki matakai kan Saudiyya

November 3, 2018

Amnesty International ta yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta tursasa Saudiyya amsa laifukan take hakkin jama'a a Yemen.

Portraitfoto: Mohammed bin Salman
Hoto: picture-alliance/AP/A. Nabil

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta tursasa Saudiyya amsa laifukan take hakkin jama'a a Yemen da ma cikin gida.

A ranar Litinin da ke tafe ne hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar ta Duniya, za ta yi zaman sake nazarin al'amuran da suka wakana a Saudiyya, a shekaru hudun da suka gabata.

Saudiyyar dai na fuskantar matsin lamba daga sassan duniya daban-daban, musamman kan kisan dan jaridar nan Jamal Khashoggi da ta yi a karamin ofishin jakadancinta da ke birnin Santanbul na kasar Turkiyya a farkon watan jiya.

Jagoran kungiyar Amnesty Int'l a yankin kasashen Larabawa, Samah Hadid, ya ce dole ne kasashe masu wakilci a Majalisar Dinkin Duniyar su kawo karshen zuba ido da suke yi a kan Saudiyya, su kuma hanzarta daukar matakai a kanta.