Amnesty ta zargi Tanzania da batar da gawarwakin 'yan adawa
December 19, 2025
Kungiyar kare hakkin 'dan adam ta duniya Amnesty International, ta zargi jami'an tsaron Tanzania da batar da tarin gawarwakin jama'a da aka kashe, a yayin zanga-zangar adawa da gwamnati.
Amnesty International ta ce jami'an tsaron sun ziyarci wuraren ajiye gawarwaki na yankunan kasar, inda suka yi awon gaba da gawarwakin, wadanda har yanzu ba a san wurin da suka kai su ba, sannan kuma akwai daruruwan mutanen da suka kama dauke da raunukan da ke bukatar kulawar likitoci, amma su ma har yanzu ba a kai ga gano inda suke ba.
A na ta bangaren, babbar jam'iyyar adawa ta Chadema, cewa ta yi mutane sama da 2,000 aka kashe, sannan aka jikkata wasu sama da 5,000, a yayin artabu da jamai'an tsaro a cikin mako guda.
Ko da yake har zuwa wannan lokaci, gwamnatin Tanzania ba ta ba da cikakken bayanin adadin mutanen da suka rasa rayukansu ba, sanadiyyar hargitsin na karshen watan Oktoban 2025.