1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taliban ta hana mata 'yancin walwala

Ramatu Garba Baba
July 27, 2022

Wani sabon rahoton Amnesty International ya gano yadda miliyoyin mata a Afghanistan ke rayuwa cikin kunci saboda yadda Taliban ke tauye musu hakkinsu.

Afghanistan Kabul | Frauen warten auf Brotausgabe
Hoto: ALI KHARA/REUTERS

Kungiyar Amnesty International ta bankado labarin yadda ake cin zarafin mata a Afghanistan. A rahoton da ta fitar a wannan Laraba, an gano yadda mata da yara mata ke rayuwa cikin tsanani saboda yadda gwamnatin Taliban ke tauye musu hakkinsu da hana su damar samun ilimi da duk wani 'yanci na walwala.

Rahoton  Kungiyar mai kare hakkin bil'adama, mai taken ''Kisan mummuke'' ya kafa hujja da zantawar da yayi da mata sama da dari da suka bayar da labarin yadda aka ci zarafinsu ta hanyar gallaza musu azaba da musu barazanar kisa, akwai wadanda aka rawaito sun yi batan dabo tun bayan da suka fito suka soki manufar gwamnatin.

Kungiyar ta ce, muddun manyan kasashen duniya suka ki daukar matakin ceto rayukan miliyoyin matan Afghanistan, to hakan na nufin an juya musu baya wanda kuma laifi ne babba na take hakkin dan adam. Kungiyar na son ganin an dauki matakin sanyawa kusoshin gwamnatin Taliban da suka kwace mulki da tsinin bindiga a bara takunkumi.