1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Amnesty: Yara na kara shiga ta'addanci a Nijar

September 13, 2021

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International, ta ce ana ci gaba da samun karuwar kananan yara da hare-haren ta'addanci ke samun su a Jamhuriyar Nijar.

Symbolbild | Amnesty: Kinder leiden unter Terror in Westafrika
Hoto: imago images/Joerg Boethling

Cikin wani rahoton da ta fitar a yau Litinin, Amnesty International ta kuma ce akwai yara kananan da dama da ake tilasta wa zama mayakan kungiyoyin masu tsattsaurar ra'ayi a iyakar Nijar da Mali da Burkina Faso.

Sama da kananan yara 60 ne suka rasa rayukansu a yankin Tillaberi da ke na Nijar, daga farkon wannan shekara zuwa halin da ake ciki.

Rahoton kungiyar ya nuna cewa rayukan mutane 544 suka salwanta a fadin Nijar sakamakon hare-hare daga ranar daya ga watan Janairu zuwa 29 ga watan Yulin bana.

Rahoton dai na zuwa ne makonni biyu bayan wasu 'yan bindiga a bisa babura sun kashe mutane 11 a garin Garba Kouara a yankin Tillaberi.