Amsoshin Takardunku :Tarihin Borno
July 17, 2023![Mun yi amfani da tsohon hoto](https://static.dw.com/image/66252039_800.webp)
Talla
Daular Borno tsohuwar Daula ce a Afirka da aka kafa tun kafin karni na 10 wacce ta hada da yankunan da yanzu ke cikin Najeriya da Nijar da Chadi da Kamaru da Sudan har Libya. Masana tarihi sun ce mutanen Saifuwa daga Yemen ne suka fara kafa daular musulunci a Borno, tsawon shekaru 1000 da suka gabata.