1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaUkraine

Amurka ba za ta juya wa Ukraine baya ba - Lioyd Austin

Abdoulaye Mamane Amadou
March 19, 2024

Gwamnatin Amurka ta bayyana anniyarta ta ba wa Ukrain dukkanin goyoyn bayan da take bukata game da mamayar da take fuskanta daga Rasha.

Babban sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin
Babban sakataren tsaron Amurka Lloyd AustinHoto: Daniel Roland/AFP/Getty Images

Amurka ta kara jaddada goyon bayanta ga Ukraine wannan kuwa duk da tangardar da aka samu na kin amincewa da wani kunshin tallafin kudin makamai daga majalisar dokokin kasar.

Da yake jawabi a yayin bude taron kasashe kawayen Ukraine a sansanin Ramstein a Jamus, babban sakataren harkokin tsaron Amurka Lioyd Austin, ya ce Amurka ba za ta juya wa Ukraine baya ba komai rintsi.

Lioyd Austin ya kara da cewa mun sha alwashin ba wa Ukraine dukkanin tallafin da take bukata domin ta jajirce daga mamayar da take fuskanta daga Rasha.