1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Amurka da Chaina na tattauna rikicinsu na haraji a London

June 9, 2025

Kasashen biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya sun rika kakaba wa juna haraji tun a watanni da suka gabata.

Shugaba Donald Trump na Amurka ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Truth Social cewa ya na sa ran tattaunawar za ta kasance salun-alun
Shugaba Donald Trump na Amurka ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Truth Social cewa ya na sa ran tattaunawar za ta kasance salun-alunHoto: Kevin Lamarque/REUTERS

Amurka da kuma Chaina suna tattaunawa bisa teburi a London don lalubo hanyar warware yakin tattalin arziki da kasashen biyu ke yi tun dawowar shugaba Donald Trump kan karagar mulki. Tattaunawar da ke gudana a yau Litinin ta kunshi Sakataren Baitul Malin Amurka Scott Bessent da na kasuwanci Howard Lutnick da kuma wakilin cinikayyar kasar Jamieson Greer.

Trump ya amince da jinkirta karin haraji kan kasashen EU

Ita kuwa Chaina, babban jami'inta da ya jagoranci tattaunawar tattalin arziki a birnin Geneva ne He Lifeng ke jagorantarta yanzu ma kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen kasar ta sanar. Shugaba Donald Trump na Amurka ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Truth Social cewa ya na sa ran tattaunawar za ta kasance salun-alun.

Chaina da Amurka za su gana kan batun kasuwanci

Sakatariyar yada labaran fadar White House Karoline Leavitt ta fada wa kafar yada labarai ta Fox News cewa suna bukatar ganin Amurka da kuma Chaina sun ci gaba da bin yarjejeniyar da aka cimma a Geneva sau da kafa.