1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Amurka da China sun amince da mayar da huldar tsaro

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
November 16, 2023

Kasashen biyu sun yi hannun riga kan batun Taiwan, bayan da Mr Xi ke cewa babu gudu babu ja da baya kan batun hade Taiwan din da China

Hoto: MFA CHINA/UPI Photo/IMAGO

Amurka da China sun amince da mayar da huldar al'amuran da suka shafi tsaro wadda ta yi tsami a baya, bayan kammala wata ganawa ta sa'o'i 4 a tsakanin Shugaba Joe Biden na Amurka da takwaransa na China Xi Jinping jiya Laraba a California, ko da yake an jiyo Mr Biden na cewa har yanzu yana kallon Shugaba Xi a matsayin dan kama-karya.

Karin bayani:Barazanar yakin cacar baki tsakanin Amirka da China

Kasashen biyu sun amince cewa China za ta taimaka wajen kawo karshen sarrafa hodar iblis ta fentanyl mai matukar hatsari da ta zama annoba ga Amurkawa.

To amma shugabannin sun yi hannun riga kan batun Taiwan, inda Mr Xi ke cewa babu gudu babu ja da baya kan batun hade Taiwan din da China, kuma lallai Amurka ta dakatar da taimaka wa Taiwan din da take yi da makamai.

Karin bayani:Chaina za ta hada hannu da Rasha don magance rikicin Gaza

Haka zalika shugabannin sun tattauna kan rikicin Gaza da kuma Ukraine, inda ra'ayoyinsu suka bambanta game da bangarorin da suke goyon baya.