Amurka da Hungary sun daidaita kan makamashi
November 8, 2025
Talla
Firaministan kasar Hungary, Viktor Orban, ya ce shugaban Amurka Donald Trump ya tabbatar masa cewa kasarsa za ta ci gaba da samun makamashi daga Rasha.
Victor Orban ya baiyana hakan ne bayan ganawarsa da Shugaba Trump a fadar White House.
Tun kafin wannan ganawar, Shugaba Trump ya nuna a fili cewa yana duba yiwuwar bai wa Hungary wani keɓantaccen matsayi, kasancewar kasar ba ta da tashar jiragen ruwa, tunda tana tsakiyar kasashe.
Wannan matakin na Trump dai ya bambanta da manufarsa ta baya, inda yake matsa wa kasashen da ke ci gaba da sayen man fetur da iskar gas daga Rasha duk da rikicin Ukraine da ke ci gaba.