1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Amurka da Iran na ci gaba da musayar makamai masu linzami

June 11, 2026

Farmakin dakarun Amurka ya shafi biranen Tehran da Bandar Abbas da wasu sannan kudanci har ma da tsibirin Hormuz.

Hoto: WANA/REUTERS

Hare-hare na zuwa bayan da Shugaba Donald Trump ya sanar da cewa Tehran za ta dandana kudarta, sakamakon jan kafa da take yi wajen cimma yarjejeniyar nukiliya da Washington DC.

Karin bayani:Isra'ila ta kaddamar da harin makamai masu linzami kan Iran

Sai dai dakarun Iran sun mai da martani ta hanyar harba rokoki da makamai masu linzami a sansanonin Amurkan da ke kasashen Bahrain da Kuwait da kuma Jordan. Sannan ta yi barazanr ci gaba da rufe mashigin ruwan Hormuz.

Karin bayani:Amurka da Iran sun sake yin musayar wuta a tsakaninsu

Musayar makamai masu linzami da rokoki da kuma luguden bama-bamai tsakanin Amurka da Iran, ya shafi tattalin arzikin duniya kama daga farashin makamashi da iskar gas da hauhawan farashin kayan masarufi har ma da sauran kayan bukatun yau da kullum.