Ko tsagaita wuta za ta dakatar da yakin Iran?
April 8, 2026
Shugaba Donald Trump na Amurka ya janye barazanarsa ta ragargaza Iran, sakamakon cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta tsawon makonni biyu da kasashen biyu suka cimma, ciki har da batun bude mashigin ruwan Hormuz.
Cimma masalahar na zuwa sa'o'i biyu, gabanin cikar wa'adin Trump na kai farmaki kan cibiyoyin lantarkin Iran da gadoji da ma rusa kasar baki-daya.
Karin bayani: Iran ta bai wa jirgin ruwan Malaysia damar wucewa ta Hormuz
Majalisar koli ta tsaron Iran ta nuna amincewarta da tayin na Amurka, wanda ta ce za ta zauna da ita a Pakistan ranar Juma'a, 10 ga watan Afirilu domin daddalewa, to sai dai Iran din da Amurka ba su tabbatar da lokacin da tsagaita wutar za ta fara aiki ba.
Iran ta amince da bude mashigin ruwan Hormuz, don bai wa jiragen ruwa masu dakon mai damar ratsawa ta ciki, wanda rundunar juyin-juya-halin kasar IRGC ta datse, a dalilin yaki da kawancen Amurka da Isra'ila.
Karin bayani:Saudiyya ta rufe gadar da ta hada ta da Bahrain saboda Iran
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce za su bude mashigin har tsawon makonni biyu, kamar yadda yarjejeniyar tsagaita wutar yaki ta nuna, to amma sai dai bisa kulawar sojojin kasar.
Karin bayani:Isra'ila ta kashe babban jami'in leken asirin Iran
A wani sako da shugaba Donald Trump na Amurka ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Truth Social, ya ce firaministan Pakistan Shehbaz Sharif ya roke shi da kada ya kai farmakin da ya kuduri aniyar kai wa ta ragargaza Iran.